Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 22/05/2016

A kwanakin baya ne aka yi wani taron koli kan yaki da cin hanci da rashawa a birnin London, kuma daya daga cikin mahalarta taron shi ne Malam Ibrahim Magu, shugaban riko na hukumar EFCC, mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.

A lokacin ziyarar da ya kai ofishinmu na London, abokin aikinmu Abdullahi Tanko Bala ya tattauna da shi, inda ya fara da tambayarsa ko nawa hukumar ta kwato ya zuwa yanzu daga wadanda ake zargi sun wawure dukiyar gwamnati?