Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 11/06/2016

A Najeriya, jama'a na ci gaba da kokawa kan matsalar hauhawar farashin kayayykin masarufi, wanda a kullum ke karuwa babu kakkautawa.

Wannan na faruwa ne yayin da a bangare guda kuma akasarin 'yan Najeriyar ke kukan matsanancin talauci, lamarin da ya kara tsananta tsadar rayuwar.

To shin mene ne ya janyo wannan matsala? Yaya 'yan Najeriyar ke tunkarar rayuwa a irin wannan yanayi? Ina kuma mafita?

A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, Wakilinmu Is'haq Khalid ya duba mana lamarin ga kuma rahoton da ya aiko mana daga Bauchi.