Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shekara 40 da zanga-zangar Soweto

A ranar 16 ga watan Yunin shekara ta 1976, dubban daliban kasar Afrika Ta Kudu, suka bazama kan titunan Soweto domin yin zanga-zangar nuna adawa da mulkin wariyar launin fata na tsirarun fararen fata.

'Yan sanda sun kashe daruruwan mutane, al'amarin da ya sauya siyasa da zamantakewar kasar.

Wakilin BBC Chris Parkinson, ya je ainihin kan titin da abin ya faro shi da wani wanda ya shaida lamarin a wancan lokacin ya kuma tsira da ransa.