Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 18/09/2016

A jamhuriyyar Nijar, hukumomin kasar sun shirya bukukuwan cika shekara 100 da haihuwar tsohon shugaban kasar marigayi Diori Hamani.

Bukukuwan da aka kammala a ranar 16 ga watan Yuni, sun bayar da damar waiwayen ayyukan da tsohon shugaban kasar ya yi a tsawon mulkinsa daga shekarar 1960-1974.

Bayan hambarar da shi dai, hukumomin mulkin soja sun daure shi a gidan kaso, sannan daga bisani aka sake shi bayan mutuwar janar Seni Kunche.

Alhaji Diori Hamani ya rasu a shekarar 1989.

A filin Gane Mani Hanya na wannan makon, wakilinmu Baro Arzika daga Yamai, ya hada mana rahoto na musamman a kan wannan biki.