Karancin ruwa ya yi kamari a birnin Kano

Image caption Jama'a na cincirindon diban ruwa

Birnin Kano da ke arewacin Najeriya ya auka cikin matsanancin karancin ruwan famfo a wannan lokaci.

Wannan al'amarin dai yasa sai mutane a wasu unguwannin birnin sun yi tafiyar kimanin kilomita daya zuwa daya da rabi domin samun masu kurar ruwa kafin su saya.

Wakilin BBC a Kano Mukhtari Adamu Bawa, ya ci karo da wani cincirindon yara dauke da bokitai da jarkoki suna turmutsutsu don samun ruwan sha da aka kawo a cikin wata motar tanki a unguwar Fagge.

Wata da ba ta samu ruwan ba a lokacin da ake rabon ta shaida masa cewa, tun farkon watan Azumi suke fama da rashin ruwan famfo.

Ta ce, ''Da kokawa fa muke samun ruwan, kuma mu mata ne za ka ga mazan sun fi karfinmu dole wani lokacin sai dai mu hakura mu uba ido sai sun gama samu tukunna, don ba za mu iya dambe da su ba.''

Mukhtari Bawa ya kuma zagaya unguwanni da dama na birnin kamar su Dorayi da Gadon Kaya da Sabon Titi da Kabara da Soron Dinki da ke tsakiyar birnin, sai kuma Rimin Kebe da 'Yan kaba Kawaji a gabashin birnin, inda ya ga yadda masu kurar ruwa suke tsere da sauran masu ababen hawa a kan tituna don kai ruwa zuwa inda ake tsananin bukatarsa.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Famfuna sun zama tamkar kayan ado don ba sa zubar da ruwa

Idris Mustapha Soron Dinki ya ce su kan yi tafiyar kilomita daya ko fiye, domin neman mai kurar ruwan da za su saya.

''Sai mun tashi daga nan Soron Dinki har zuwa Goron Dutse kafin mu samo mai kurar ruwan da za mu saya a wajensa,'' in ji Idris.

Duk da cewa wasu ungwannin suna da famfunan tuka-tuka, amma ta'azzarar matsalar rashin ruwan yasa masu diba su kan bata dogon lokaci kafin su diba saboda dogayen layuka.

Wakilin BBC ya ce ya ziyarci wani famfon tuka-tuka a unguwar Dandago, inda wasu matasa da yara suka jera jarkoki domin dibar ruwa.

Wasu unguwannin sun ce matsalar rashin ruwan ta dade tana ci musu tuwo a kwarya. Yayin da wasu kuma ke cewa a baya-bayan nan ne karancin ruwa ya ta'azzara.

Abin tambayar shi ne, ko a ina masu kurar ruwan suke samo ruwan da suke sayarwa a jarkoki?

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A wasu lokutan mutane basu da zabi sai amfani da ruwan da ba tsaftatacce ba

Ga abin da wani mai kurar ya shaida wa wakilin BBC, ''Muna samo ruwan ne a wasu unguwanni masu nisa da basu cika fama da matsalar ba, amma gaskiya tura ruwan yana da wahala musamman ga azumi a bakinmu kuma. Muna dai yi ne domin neman na rufin asiri.''

Manajan daraktan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano Auwalu Muhammad Galadanci, ya alakanta matsalar karancin ruwan da rashin wutar lantarki da kuma man dizel.

Image caption Gwamnatin jihar Kano ta ce tana bakin kokarinta don shawo kan lamarin

Matsalar karancin ruwa na tilasta mutane yin amfani da na kafofi marasa tsafta, wanda hakan abu ne mai matukar illa ga lafiyar jama'a musamman ma dai birni mai cunkushe da al'umma irin Kano, wanda kuma ake yawan samun annobar cutar amai da gudawa da sauran cututtuka masu alaka da ruwa mara tsafta.