Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kungiyoyin addini sun taimakawa marayu

A Najeriya, yayin da watan azumin Ramadan ya zo karshe, jama'a da kuma kungiyoyi na cigaba da kokarin tallafa wa marasa galihu, a lokacin da ake fama da matsin tattalin aziki.

A jihar Lagos da ke Kudancin kasar, wasu kungiyoyin addini sun fara rabawa marayu sama da 500 tufafi kyauta.

Kungiyar Izalatul Bid'ah Wa Ikamatussunah da kuma wasu daga shugabannin addini ne su ka bullo da wani shirin da zai taimaka wajen ilimantar marayu kyauta.

Ustaz Umar Lawan Atna, shi ne shugaban kwamitin rarraba kayayakin ga marayun, ga kuma bayanin da ya yi: