Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya: Tsaro a yankin Diffa - 16/07/2016

Baya ga Najeriya, za a iya cewa Jamhuriyar Nijar wadda ita ce makwabciyar Najeriyar ta kusa, ta kasance kasa ta biyu da ta fuskanci hare-haren kungiyar Boko Haram, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan kasar da suka hada da fararen hula da sojoji, baya ga dumbin mutanen da hare-haren suka daidaita.

Duk da cewa kasar ta sha fadin cewa tana iyakacin kokarinta wajen tunkarar matsalar, amma wasu na ganin cewa har yanzu gwamnati ba ta yi shirin dakile hare-haren ba sakamakon gaza sama wa sojoji isassun makamai na zamani.

A filin Gane Mani Hanya na wannan makon, wakilinmu Baro Arzika, ya yi duba kan yanayin da ake ciki musamman a yankin jihar Diffa wadda ta yi fama da hare-haren 'yan Boko Haram, ga kuma rahoton da ya hada mana: