Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Irmiya na son zama babban dan kasuwa

Irmiya Ishaya matashi ne mai shekara 18, ya ce ba shi da burin da ya wuce zama babban dan kasuwa, tare da bude manyan kamfanoni domin daukar matasa aiki.

Ya yi wa shirin BBC Hausa na ''Burina,'' bayani kan yadda yake son wannan buri nasa ya cika.

Ku ma za ku iya turo mana bidiyo ko muryar da kuka nada ta lambarmu ta WhatsApp 08092950707.