Shugabannin manyan jamiyyun Burtaniya sun yi mahawarar karshe

Shugabannin manyan jamiyyun Burtaniya sun yi mahawarar karshe
Image caption Shugabannin manyan jamiyyun Burtaniya sun yi mahawarar karshe

Shugabannin manyan jama'iyu ukku na Birtaniya sun yi muhawararsu ta ukku, kuma ta karshe a Talbijin gabanin babban zaben da za'a yi a mako mai zuwa.

Piraministan Burtaniya, Gordon Brown da shugaban jam'iyyar Conservative, David Cameron da kuma na jama'iyyar Liberal Democrats, Nick Clegg sun yi muhawarar ne akan batun tattalin arziki, da kuma yadda za a rage gagarumin gibin da Birtaniya take fama da shi.

Shugaban jam'iyyar Conservative, David Cameron ya ce ba zai taba barin Burtaniya ta shiga sahun kasashe masu amfani da kudin Euro ba kuma ya yi gargadin kar a kuskura a tallafawa kasashen turai da tattalin arzikinsu ke cikin matsi irin su Girka.

Firaminista Gordon Brown kuwa na jam'iyyar Labour cewa ya yi shi ya nuna kwarewa wurin tafiyar da tattalin arzikin kasar cikin lokacin yalwa da lokacin kunci.

A yayinda Nick Clegg ya sake gabatar da jamiyyar sa ta Liberals democrats a matsayin jamiyyar da zata kwatanta adalci idan an zabe ta .