An rantsar da Goodluck Jonathan a matsayin shugaban Najeriya

Goodluck Jonathan
Image caption Sabon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A Najeriya, da safiyar ranar alhamis biyar ga watan Mayu ne aka rantsar da mukaddashin shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan a matsayin shugaban kasa.

An rantsar da shugaban kasar ne bisa tanadin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi cewa a gaggauta rantsar da mataimaki da zarar an rasa shugaban kasa sakamakon mutuwa ko wasu manyan dalilai.

Sabon shugaban kasar dai ya sha alwashin cika alkawuran da suke yi wa `yan Najeriya tare da magabacinsa tun lokacin neman zabe, musamman wanzar da zaman lafiya a yankin Niger-Delta da kuma inganta harkar zabe.

Mukaddashin shugaban Najeriya, Dokta Goodluck Jonathan ya yi shan rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa bisa jagorancin Babban mai shara`ar kasar, Aloysious Katsina Alu.

Bidiyon rantsar da Goodluck Jonathan

Bayan ya sha rantsuwar ne ya gabatar da jawabi inda ya jaddada aniyarsa ta cika wa `yan Najeriya alkawarin da suka tare da marigayi, shugaba Umaru Musa `yardua na inganta rayuwar jama`a.

Ya ce; "za mu ci gaba da irin dukufar da muka yi wajen samar da shugabanci nagari, da inganta harkokin zabe da kuma yaki da cin hanci da rashawa ba kakkautawa. Kuma mun sha fada cewa wajibi ne mu inganta tsarinmu na zabe ta yadda `yan kasa za su ga tasirin kuri`un da za su kada a babban zaben kasar na badi".

Kazalika, shugaban ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da kokarin da ya ce tana yi wajen wanzar da zaman lafiya a yankin Niger-Delta da kuma kasar baki daya.

Wasu `yan Najeriyar da dama dai sun yi tsammanin cewa a wajen rantsarwa ne shugaban kasar zai fadi sunan wanda zai kasance masa mataimaki, wanda kuma ake sa ran cewa zai fito daga bangaren arewacin kasar.

Amma har ya kammala jawabinsa bai tabo wannan batun ba.

Kundin tsarin mulkin Najeriya dai ya yi tanadin gaggauta nada mataimaki ya zama shugaban kasa a irin wannan yanayi da Allah ya karbi shugaban kasar, amma bai wajibta rantsar da sabon shugaban tare da wanda zai yi masa mataima ba.

Nada Mukadashin Shugaban kasa

A farkon watan Fabrairun shekarar 2010 ne mataimakin shugaban kasar Goodluck Jonathan ya zama mukaddashin shugaban kasa, bayan ce ce kucen da ake tayi na tafiyar shugaban kasar, wanda ya yi batare da mika ragamar mulki ga mataimakin nasa ba.

Majalisun dokokin kasar ne dai suka tabbatar da Goodluck a matsayin mukuddashin shugaban kasa, a yayinda suka yi amfani da Hirar da BBC tayi da shugaba Yar'Adua a matsayin sanarwa da majalisar cewar yana jinya.

Majalisun biyu dai sun ce duk sanda Yar'adua ya dawo kasar kuma ya rubuto mata cewar zai ci gaba da aikinsa, sannan ragamar mulki za ta koma hanunsa.

Ana cikin rudani da kuma rashin tabbas game da halin da shugaban kasar ke cikin ne, BBC tayi hira da shi ta wayar tarho, inda ya ce, yafara samun sauki kuma idan likitocinsa sun sallame shi zai dawo gida ya ci gaba da aikinsa.

Hirar Yar'adua da BBC

'Ban yi magana da Shugaban kasa ba'

Mista Goodluck Jonathan a wata hira da ya yi da BBC a Amurka a watan Afrailu ya ce bai yi magana, kuma bai gana, da Shugaban kasa Alhaji Umaru 'Yar'aduwa ba tun bayan da shugaban kasar ya koma gida watanni uku da suka wuce.

"Ina tsammanin ya bar Najeriya da duku-dukun ranar 24 ga watan Nuwamba, sai kuma ranar 26 muka yi magana mai dan tsawo".

Bidiyon hirar Mista Goodluck Jonathan

"Tun bayan nan dai ba mu sake wata doguwar tattaunawa ba".

Mukaddashin Shugaban kasar ya ce bai samu ganin Shugaba 'Yar'adua ba tun bayan komawarsa Najeriya kusan watanni biyu da suka wuce, kuma bai yi magana da shi ba.