Burtaniya za ta sa ido a zaben Najeriya

Gwamnatin Birtaniya ta gayyaci sakataren hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta da wasu 'yan Majalisun dokokin kasar don sa ido akan zaben da ake shirin gudanarwa a kasar a wannan makon.

Su dai wadanda aka gayyata zasu je ne, a matsayin yan kallo har zuwa lokacinda za'a kammala zaben.

Masu sanya ido a zabubbukan dai, musanman ma a kasashen yammacin duniya, na taka muhumimmiyar rawa wajen tabatar da ingancin zabe.