An gurfanar da Faisal Shahazad

Faisal Shahadaz
Image caption Mista Shahadaz ya amsa duk laifin da ake tuhumarsa da shi

Dan Amurkar nan dan asalin kasar Pakistan Faisal Shahzad, an gurfanar da shi gaban kuliya bisa zarginsa da yunkurin tada bam din da bai yi nasara ba a dandalin Times Square dake birnin New York a ranar asabar.

Zarge zargen da ake masa sun hada da yunkurin yin amfani da makamin kare dangi da kuma yunkurin kashe mutane ta hanyar ta'addancin kasa da kasa.

Hukomomin kasar sun ce wanda ake zargin ya amsa aikata laifi.

Sai dai dai ba'a bayana ranar da kotun zata fara sauraran karar ba, saboda kawo yanzu wanda ake zargin na cigaba da amsa tamboyoyi kuma masu gudunar da bincike dake Amurka sun maida hankalinsu kan kussancin sa da wasu yan gungun mau tada kayar baya dake kasashen waje saboda, ya shafe watanni kussa da biyar a kasar Pakistan a bara.