Jonathan na cigaba da tuntuba

Jonathan
Image caption Har yanzu Shugaba Jonathan bai zabi mataimakinshi ba

Mahukunta a Najeriya sun bayyana cewa, har yanzu gwamnati bata kammala tuntubar masu ruwa da tsaki ba, don yanke shawara akan wanda za a nada a matsayin mataimakin shugaban kasar.

Jama'a a Najeriyar dai sun matsu su ji sunan wanda shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan zai nada, a matsayin mataimakin sa.

A hirar da yayi da BBC, minista a ma'aikatar yada labarai ta Najeriyar, Mr. Labaran Maku, ya ce shugaban kasar na ci gaba da tuntubar shugabannin addinai da na siyasa, kuma nan bada jimawa ba zai bayyana sunan wanda za'a nada.

A makon jiya ne dai aka rantsar da Dr Goodluck Jonathan a matsayin shugaban kasar, bayan rasuwar shugaba Umaru Musa 'Yaradua.