Rarrabuwar kawuna akan Pfizer a Kano

Tuta
Image caption Tutar Najeriya

Kungiyar masu neman diyya daga kamfanin Pfizer, wanda yayi gwajin wani maganin sankarau a Kano a 1996, sun ce sun janye daga yarjajeniyar sasantawa a wajen kotu, tsakanin gwamnatin jahar Kano da kamfanin, kan batun biyan diyya ga wadanda abin ya shafa.

Kungiyar tace ta dauki wannan mataki ne, sakamakon rashin gamsuwa da yadda kwamitin amintattun biyan kudin ke gudanar da ayyukan tantance wadanda suka cancanci a biyasu diyyar.

Wa'adin kammala aikin da aka ba kwamitin amintattun ya cika a watan Disambar bara. An dai yi zargin cewa gwajin da kamfanin Pfizer ya yi, ya janyo hasarar rayuka da nakasa a jahar ta Kano.