Rasuwar Shugaba Umaru Musa Yar'adua

Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar'adua
Image caption Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar'adua

Allah yayi wa tsohon shugaban Najeriya, Alhaji Umaru Musa Yar'adua rasuwa ne a daren ranar talata 5 ga watan Mayus bayan wata 'yar doguwar jinya.

Tashar talibin ta tarayar dake kasar, ta ce mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro, Janarar Aliyu Gusau shine ya sanar da mukaddashin shugban kasan Najeriyar, dakta Goodluck Jonathan da rasuwar sa.

Shugaban Najeriya Umaru Musa `Yar'adua shi ne shugaba na biyu da ya karbi ragamar mulkin kasar bayan komawarta ga turbar Demokuradiyya a shekarar 1999.

Kuma ya karbi ragamar mulki ne daga hannun shugaba Olusegun Obasanjo bayan wani zabe mai cike takaddama a shekara ta dubu biyu da bakwai.

Bayanin rasuwar shugaban na Najeriya Umaru Musa Yar 'Adua ya jefa kasar cikin wani hali na tunani game da salon da batun mulki da kuma harkokin siyasar kasar za su dauka.

Takaitaccen tarihin marigayi

An haifi marigayi tsohon Shugagan na Najeriya, Mallam Umaru 'Yar'adua ne ranar 16 ga watan Agusta na shekarar 1951.

Mallam Umaru Musa 'Yar'adua ya fara karatu ne daga makarantar Rafuka a 1958, daga nan har ya yi babban digirinsa a fannin nazarin kimiyar harhada sinadarai.

Farkon aikin da ya yi shi ne na Mallanta a makarantar Holy Child da ke Lagos. Duk da yake marigayin ya yi aiki a kamfanoni da dama, aiki guda da ya fi kankama a tsawon rayuwarsa na hamsin da tara shine aiki Mallanta.

A jamhuriya ta biyu, Mallam Umaru Musa 'Yar'adua ya yi jam'iyyar PRP, sanan kuma a shekarar ta 1999, lokacin da demokradiyya ta dawo Najeriya, marigayin ya yi takarar mukamin gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Katsina kuma ya ci, mukamin da ya zarce a kai a zuwa shekara ta 2003.

Sai dai ba wannan ba ne karo na farko da ya tsaya takarar gwamna a jihar, a shekarar 1991, Marigayi Umaru 'Yar'adua ya yi takaran kujeran gwamnan a karkarshin inuwar jamiyyar SDP, inda ya sha kaye a hannun Sa'idu Barda na jamiyyar NRC.

Marigayi Umaru Musa 'Yar'adua shi ne gwamna na farko da ya fara bayyana kadarorin daya mallaka a fili, kamar yadda doka ta bukata a Najeriya.

Ya kuma kasance gwamna na biyar da ya kaddamar da Shari'ar musulunci a jihohin arewacin Najeriya.

Marigayi Umaru Musa `Yar'adua ne shugaba na biyu da ya karbi ragamar mulkin kasar bayan komawarta ga turbar Demokuradiyya a shekarar 1999.

Kuma ya karbi ragamar mulki ne daga hannun Shugaba Olusegun Obasanjo bayan wani zabe mai cike takaddama a shekara 2007.

Marigayi Umaru Musa 'Yar'adua ya rasu ne ya bar mai dakinsa, Hajiya Turai da 'ya'ya biyar mata da biyu maza. Ya kuma taba auren Hajiya Hauwa Umar tsakanin 1992 da 1997, kuma sun haifi 'ya'ya biyu maza.

Ta'aziya

Samun sanarwar rasuwar shugaba Umaru Musa Yar'adua ke da wuya, sai Shugaban Amurka, Barrack Obama, ya fito ya bayyana ta'azziyarsa, inda ya ke cewa; "zamu dunga tunawa tare da girmama, irin mutunci da kuma kamun kan da marigayi Shugaba 'Yar'adua ke da shi, tare da tsananin sadaukar da kai ga yiwa kasa aiki, da kuma imanin da yayi da irin dumbin albarkatun da Allah yayiwa kasarsa, da kokarin samar da kyakkyawar makoma ga al'umar Nigeria miliyan dari da hamsin".

Shugaban na Amurka ya ce a karkashin shugabancin marigayi 'Yar'adua, Nigeria da Amurka sun dauki matakai na kyautata dangon zumunta dake tsakanin kasashen biyu, kuma wannan aikin shine ya ci gaba, ko a cikin 'yan watannin bayan nan, a lokacin da rashin lafiya ta ci karfin shugaban daga gudanar da harkokin mulkiShi kuwa shugaba Boni Yayi na jamhuriyar Bene ya bayyana cewa ne, ya yi asarar babban amini.