Yan Najeriya sun bayana nasarorin marigayi Umaru Musa Yaradua

Tsohon shugaban Najeriya Marigayi Umaru 'Yar'adua
Image caption Tsohon shugaban Najeriya Marigayi Umaru 'Yar'adua

A Najeriya, yayin da aka shiga rana ta biyu na zaman makokin rasuwar marigayi Alhaji Umaru Musa Yar'adua, yanzu haka wasu da dama a kasar na ci gaba bayyana irin nasarorin da suke ganin tsohon shugaban kasar ya cimma a lokacin da yake mulkin kasar, duk kuwa da matsalolin da wasu ke ganin gwamnatinsa ta fuskanta.

Honorable Sada Soli Jibiya `dan Majalisar wakilai Najeriyar, ya shaidawa BBC cewa Alhaji Umaru Musa Yar'adua ya kawar da duk wata kiyayya a zukatan wadanda ke adawa da salon mulkin tsohon shugaban kasar.

Ya kuma ce marigayin, ya gudunar da wasu ayyukan cigaban rayuwa a kasar, wadanda suka hada da yashe kogin kwara da kuma shirin yin afuwa ga masu tada kayar baya a yankin Niger Delta mai arkin mai.

A jiya ne dai aka gudunar da janaizzar tsohon shugban kasar a jihar Katsina dake Arewacin Najeriya.

Kasashen Ghana da kuma jamhuriyar Niger sun mika sakon ta'aziyar su ga yan Najeriya dangane da rasuwar Alhaji Umaru Musa Yar'adua.