David Cameron ne sabon Pirayi Minista

David Cameron
Image caption Jam'iyyar Consevatives na David Cameron ta samu mafi rinjayen kujeru a majalisar Birtaniya

Shugaban Jam'iyyar Conservatives a Birtaniya David Cameron ya zama sabon Pirayi Ministan Birtaniya.

Hakan ya biyo bayan amincewar Sarauniyar Ingila Elizabeth na ya kafa sabuwar gwamnati bayan ganawarsu a fadarta na Buckingham.

Cameron ya kasance Pirayi Minista mafi karancin shekaru cikin shekaru dari biyu daya da zai kafa gwamnati.

Shi kuwa tsohon Pirayi Ministan Birtaniya Gordon Brown ya yi murabus ne abinda kuma ya kawo karshen mulkin jam'iyyar Labour na tsawon shekaru goma sha uku bayan da jam'iyyar Labour ta sha kaye a zaben da aka gudanar a makon daya gabata.