Gordon Brown ya yi murabus

Brown
Image caption Brown yayi murabus saboda jam'iyyar Labour ta sha kaye a zaben da aka gudanar makon daya gabata

Pirayi Ministan Birtaniya Gordon Brown ya yi murabus, abinda kuma ya kawo karshen mulkin jam'iyyar Labour na tsawon shekaru goma sha uku.

Ana saran shugaban jam'iyyar Conservatives David Cameron zai tafi fadar Sarauniyar Ingila nan bada jimawa ba don Sarauniya ta nadashi a matsayin sabon Pirayi Ministan.

Jam'iyyar Conservatives dai ta zamo babbar jam'iyya a kasar bayan da aka kammala zabukan makon daya gabata duk da cewar bata samu gaggarumin rinjaye ba a majalisar dokoki.

Jamiyyar Liberal Democrats a Birtaniya ta bayyana cewa idan an jima a yau talata ne za ta bayyana jamiyya daya daga cikin jamiyyun Labour da na Conservatives wadda za ta hada kai da ita domin kafa gwamnati.

Jamiyyar ta gudanar da tattaunawarta ta farko a hukumance tare da jamiyyar Labour bayanda shugabanta, kuma Piraministan kasar Gordon Brown ya bayyana aniyarsa ta sauka daga mukaminsa cikin watanni masu zuwa.

Wakilin BBC ya ce Gordon Brown yayi karfin hali, ba kawai don tabbatar da jamiyyar Labour akan karagar mulki ba, har ma da sauya fasalin siyasar Birtaniya, ta hanyar hadin gwiwar da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu.