Jonathan zai zabi mataimakinshi-Ameachi

JonathanGoodluck
Image caption Jonathan bai zabi mataimakinshi ba kwanaki shida da rantsar dashi

Gwamnan Jihar Rivers, Mr Rotimi Amaechi ya musanta cewar gwamnonin Jam'iyyar PDP karkashin inuwar Kungiyar nan da ake kira Governors Forum na matsin lamba ga Shugaban kasa, Dr Goodluck Jonathan, akan ya nada daya daga cikin gwamnonin Jam'iyyar PDP a matsayin mataimakin Shugaban kasa.

A cikin wanann makon ne dai ake sa ran Shugaban kasar zai gabatar da mutumin da zai kasance mataimatakin shugaban kasa ga majalisun dokokin kasar domin neman amincewarsu.

Tuni dai bangarori daban daban suke yayata sunayen wasu mutane da suka hada da gwamnonin wasu jihohi a matsayin wadanda ake cewar ana matsawa shugaban kasar lambar ya zaba daga cikin su.