Majalisar dokokin Najeriya tayi zama na musamman don girmama 'Yar'adua

Marigayi Shugaba Umaru 'Yar'adua
Image caption Shugaba Umaru Musa 'Yar'adua ya rasu ranar laraba shida ga watan mayu.

Majalisar dokokin Najeriya ta yi wani zama na musamman a yau, domin yin jawabai na girmama marigayi shugaba Umaru Musa 'Yar'adua, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Larabar da ta gabata, bayan ya dade yana fama da rashin lafiya.

A lokacin zaman da majalisar dattawa da ta wakilai suka yi, kowace a nata bangaren, 'yan majalisun sun yi jawabai daya bayan daya, na yabawa marigayin, kan irin abubuwan da yayi na cigaban Najeriyar, tare da bada shawarwari kan yadda za a iya karrama shi.

Wannan ne karon farko da ake cewar an gudanar da irin wannan zama kan wani shugaban kasa da ya rasu a Najeriyar.