An kafa sabuwar gwamnati a Burtaniya

clegg
Image caption Pira Ministan Burtaniya David Cameron da mataimakinsa Nick Clegg

Sabon Pira Ministan Burtaniya David Cameron ya fara nada ministocin sabuwar gwamnatin da yake kafawa wadanda suka hada da 'ya'yan jam'iyyar sa ta Conservative da kuma na Liberal Democrats.

Wannan dai shi ne karo na farko tun yakin duniya na biyu da aka kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin jam'iyyar Conservative da ta Liberals.

Ya mika manyan mukamai uku da suka hada da cansilan exchequer da Sakataren harkokin waje da na cikin gida ga 'ya'yan jam'iyyarsa ta Conservative. Shugaban jam'iyyar Liberal Democrats Nick Clegg, ya zamo mataimakin Pira minista, yayinda 'ya'yan jam'iyyarsa hudu za su samu mukamin ministoci.

Sabon Pira Ministan yace fatansa shi ne na sauya alkiblar siyasar Burtaniya. Yayinda mataimamkin nasa ke cewa gwamnatin za ta dore duk da banbacin da ke tsakanin su. Wadanda aka nada

Sabon Cansilan, George Osborne, shi ne mafi kusanci ga sabon Pira Ministan, yayinda sabon sakataren harkokin waje William Hague, nan daya daga cikin tsaffin shugabannin jam'iyyar Conservative biyu da suka samu mukamin ministoci.

Dayan shi ne Ian Duncan-Smith, wanda ya shirya rahoton da yan taimakawa jam'iyyar wajen manufofinta na zaman takewa.

Teresa May, ta zamo mace ta biyu da ta shugabanci ma'aikatar cikin gida, yayinda Liam Fox, shi ma na Conservative ya zamo sakataren tsaro.

Sai dai jama'ar kasar da dama na bayyana ra'ayoyi da suka sha banban da juna.

Manufofi

Alamu na nuna cewa kowacce daga cikin jam'iyyun za ta rasa wasu daga cikin manufofinta, amma sai dai jam'iyyarb Conservative wacce ke kan gaba a yawan kujeru za ta yi tasiri wajen alkiblar da gwamnatin za ta fuskanta.

Amma dole sai anyi taka tsantsan muddum ana son kawancen ya dore, kamar yadda jami'an bangarorin biyu suka sha nana tawa.

Ita dai Conservative babban burinta shi ne na rage kudaden da gwamnati ke kashewa, da kuma haraji.

Yayinda Lib Dems ke fatan ganin an aiwatar da sauye-sauye a fagen zaben kasar.

Banbace bance

A bangare guda dangane da manufofin harkar waje da kuma tsaro, wadannan na daga cikin abubwan da abokan hadin gwuiwar biyu wato Conservatives da Liberal Democrats suka fi baiwa karfi.

Sai dai idan ana batun tarayyar turai, 'yan Conservatives ba sa ra'ayin haka, yayinda su kuma 'yan Jamiyyar Liberal Democrats ke son hada kai da kungiyar tarayyar turai.

Kan batun tsaro kuma 'yan Liberal da dama na son a janye jirgin ruwan yakin Birtaniya wato Trident wanda ke karkashin ruwa, yayinda su kuma Conservatives ke ganin Trident din a matsayin ginshiki mai mahimmanci a harkar tsaron Birtaniya.

Sai dai an hakikance wadannan banbance banbancen ba za su dakatar da komai ba. Domin dai Gwamnati na da iyaka akan abubuwan da ta bayyana cewa za ta yi a yakin neman zabenta.