Kotu ta bada belin El Rufa'i

el rufa'i
Image caption Tsohon ministan birnin tarayyar Najeria Nasir El Rufa'i

Wata babbar kotu a Abuja ta bayar da belin tsohon ministan birnin tarayya Malam Nasiru El Rufai.

Hakan ya biyo bayan karantawa shi Malam Nasir El Rufai wasu laifuffuka takwas da ake tuhumar shi tare da wasu mutane biyu da aikatawa na daukar filayen wasu su baiwa wasu.

Dukkan su dai sun yi watsi da laifufukan da aka tuhume su da aikatawa don haka lauyoyin su suka nemi a basu beli.

Kotun ta bayar da belin mutanen uku ne kan kudi naira million dari kowannensu. Haka kuma za su gabatar da masu tsaya masu wadanda za su mallaki kadara ta fili.

Takaddama

Malam Nasiru El Rufa'i ya dade yana fuskantar kalubale daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC wacce ta zarge shi da aikata ba daidai ba lokacin da yake ministan raya birnin tarayya.

Har ila yau kwamitin majalisar dattawan kasar ma ta same shi da makamancin wannan laifi, abinda wasu ke zargin shi ne ya sa shi ficewa daga Najeriya zuwa kasar Amurka.

Takaddamar ta kai ga hukumar bayyana shi a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Amma ya dawo Nijeriya ne kusan makonni biyu da suka gabata kuma ya gabatar da kansa ga hukumar EFCC.