Majalisar ministocin Najeriya ta karrama marigayi 'yar'adua

Goodluck Jonathan
Image caption A makon da ya gabata ne dai Allahi ya yiwa 'Yar'adua rasuwa

Majalisar ministocin Najeriya ta yi wani zama na musamman a yau domin tunawa da tsohon shugaban kasar, marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yaradua.

Shugaban Nijeriyar na yanzu, Dr Goodluck Jonathan ne ya jagoranci zaman, inda suma ministoci suka nuna alhinin su.

Haka kuma Dr. Goodluck Jonathan ya bada umarnin cewa a sanyawa wani babban titin hanyar filin zirga zirgar jiragen sama na Abuja zuwa cikin gari, sunan tshohon shugaban kasar.

Tsohon shugaban kasar Ghana, John Kuffour yana daga cikin manyan bakin da suka halarci zaman majalisar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai Allah ya yiwa shugaba 'yar'adua rasuwa bayan ya yi fama da doguwar jinya.

Alhini

Daya bayan ministocin sun bayyana alhininsu ga marigayin, suna bayyana yadda mu'amilla ta kasance a tsakaninsu lokacin da yana raye.

Sakataren gwamnatin tarayya Alhaji Yayale Ahmed, ya bayyana marigayin da cewa mutum ne mai hazaka, da bin doka da oda.

Sannan yace yayi kokari wajen kawo karshen matsalar wutar lantarki da ta dabai baye kasar.

Shi ma anasa batun, ministan kula da harkokin 'yan sanda Alhaji Adamu Maina Waziri ya ce shugaba 'Yar'adua mutum ne wanda ya zama wajibi a yaba masa.

Anasa bangaren ministan kula da harkokin waje, Dakta Aliyu Idi Hong, cewa su kansu masu adawa da shugaban lokacin da yana da rai sun san yana da kyawawan manufofi.

Shi ma ministan babban birnin tarayya Sanata Bala Muhammad, ya ce shi ne na farko da ya bada kwangilar gina titi mai layi goma a kasar, kuma don haka suka nemi a sanyawa hanyar sunansa.