'Yan Najeriya sun soki tsarin karba karba

Tutar Najeriya
Image caption Kungiyoyin dai sunyi korafin cewa mulkin karba karba ba ta dace da demokradiyya ba

A Najeriya, jama`a da kungiyoyin farar-hula na ci gaba da sukar tsarin shugabanci na karba-karba da jam`iyyar PDP mai mulkin kasar ta amince da shi.

A yanzu dai kungiyar Save Nigeria Group ita ma ta ce tsarin ya saba da akida irin ta demokuradiyya.

Sai dai jam`iyyar PDP ta jaddada cewa tsarin yana da fa`ida, saboda zai baiwa kowane bangaren kasar damar shiga a dama da shi a cikin al`amuran shugabanci.

Ammah kuma wasu masu sharhi sun shaidawa bbc cewa wanan tsari na wani bangare ya baiwa wani bangare bai taso ba