Zamu samar da tsayayar gwamnati - Cameron

David Cameron
Image caption Sabon Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron

Sabon Firayim Ministan kasar Burtaniya David Cameron ya ce hadin gwiwar da jamiyyarsa ta Conservative ta kulla tare da jamiyyar Liberal Democrats, za ta iya samar da gwamnati mai karfi.

Ya ce gwamnatinsa za ta bullo da sauyen sauyen da Burtaniya ke bukata, domin fuskantar matsalolin da suka addabi kasar.

Shi kuwa jagoran jamiyyar ta Liberal Democrat wato Nick Clegg, wanda a halin yanzu shune mataimakin PM, ya ce suna kokarin kafa sabuwar gwamnati.

Ya ce Ina fata wannan shine mafarin sabon tafarkin siyasa, wanda na dade da yin imani da shi. wato mai fadi wanda yan siyasa masu akidoji iri iri za su hadu, ba tare da yin la'akari da banbance banbancensu ba, domin samar da ingantacciyar gwamnati ga daukacin kasar.

A yarjejeniyar da suka cimma jamiyyar Liberal Democrats ta sami mukaman siyasa biyar , wanda ya hada da mukamin mataimakin Firayim ministan