An kashe mutum daya a Bangkok

Bangkok
Image caption Yadda sojoji ke harbin masu zanga zanga a Bangkok

Sojoji a Bangkok, babban birnin kasar Thailand, sun bude wuta akan masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati, a lokacin farmakin da suka kai domin killace wani yanki, inda masu zanga zangar suka yi kaka gida.

An kashe wani mai zanga zanga guda daya, sannan wani sojan da ya bijirewa gwamnati, Manjo Janar Khattiya Sawadispol, wanda yake baiwa masu zanga-zangar shawara kan yadda ake daukar matakan tsaro, yana daga cikin wadanda suka jikkata.

Masu zanga zangar sun mamaye wani yanki na birnin Bangkok, sama da watanni biyu suna neman gwamnati ta sauka, domin a gudanar da sabon zabe.