Sojin Nijer sun haramta kungiyar Inganci

Salou
Image caption Shugaban Mulkin Sojin Nijer Salou Djibo

Hukumomin mulkin sojan Niger sun haramtawa kungiyar INGANCI, mai ikirarin kare demokradiyya, gudanar da ayyukanta.

Tsohon ministan sadarwar kasar, kuma kakakin gwamnatin shugaba Mamadou Tanja da sojoji suka hambarar, Malam Moctar Kassoum, shine ke jagorantar kungiyar.

Hukumomin sojan na zarginsa da faye yin kiraye kirayen a sako tsohon shugaban kasar, Malam Mamadou Tanja.

Malam Moctar Kassoum ya ce lauyansa zai shigar da kara kotu, domin neman a soke haramcin da aka yi wa kungiyar tasa.