Obama ya nemi akafa doka domin kare muhalli

Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaba Obama ya ce, yana son a kafa wata doka wadda za ta tursasawa kamfanin mai na BP ya biya dukkanin asarar da aka tabka sakamakon tsiyayar mai a tekun Mexico.

Ya aikewa majalisar dokokin kasar wasika inda yake cewa ba zai lamun cewa duk wani yunkuri na taimakawa wadanda alamarinda ya kira gagarumi, kuma balain da za a iya kaucewa na muhalli ya shafa ba.

Wakilin BBC ya ce wasikar shugaba Obama'n ta kunshi cewa gwamnati za ta yi duk iyawar ta na ganin cewa an biya diyya mai tsoka.

Kuma akan haka ne za a kara adadin da aka warewa kamfanoni su biya ida irin haka ta afku.

A watan da ya gabata ne wata farfajiyar hakar mai ta fashe a tekun Mexico, abinda ya janyo malalar mai tare da yin barazana ga wasu jihohin Amurka.