An yi harbe harbe a Bangkok

Soji a Bangkok
Image caption Sojoji da bindiga a Bangkok

Anji harbe harben bindiga a Bankok babban birin Thailand, kusa da inda masu zanga zangar kin jinin gwamnati suka shafe makwanni suna yada zango.

Haka kuma rahotanni na cewa wasu abubuwa sun fashe a wata babbar magamar hanyoyi, 'yan sa'oi bayan wa'adin daka gwamnati ta dibawa masu zanga zangar ya kare.

An kai wadanda suka ji raunuka asibiti, ciki har da jagoran zanga zangar wanda rahotanni ke cewa an harbe shi a ka.

Kakakin sojin kasar ya ce, za'a rufe wurin baki daya sannan za'a hana motoci da bas bas da jiragen kasa da kuma jiragen ruwa zirga zirga.