Ra'ayi Riga: Ci da gumin yara

wasu yara na aikin lebura
Image caption Ci da gumin yara abu ne da ya zama ruwan dare a kasashe masu tasowa.

A farkon wannan makon ne aka gudanar da taron kasashe a birnin Hague, kan yadda ake tilasta wa kananan yara yin aikace-aikacen karfi.

Mahalarta taron sun kwashe kwanaki biyu suna tattaunawa akan matsalar, a karkashin jagorancin asusun kula da kananan yara na UNICEF, da kuma kungiyar kwadago ta duniya, ILO.

A taron na Hague an gabatar da wani rahoton da kungiyar kwadagon ta wallafa, a wanda ke neman a gaggauta daukar matakan kawo karshen daukar kananan yara aiki.

Rahoton yayi tsokaci akan halin da ake ciki a yankin Afirka na kudu da hamadar Sahara, inda matsalar ke cigaba da karuwa, fiye da ko'ina a duniya.

Binciken da kungiyar kwadago ta duniya ILO ta gudanar dai na nuna cewa wannan matsala na ci gaba, ana cewar a shekara ta 2004 akwai yara miliyan 49 dake cikin wanann hali, amma shekaru hudu bayan haka sai adadin ya karu da yara miliyan goma.

To ko me ke kawo wannan matsala, kuma ta yaya za a magance ta?

Mun tattauna kan wannan batu, da Alhaji Muhammed Babandede, Darakta a hukumar NAPTIP ta Nijeriya, wadda ke yaki da safarar jama'a , da kuma Malam Sama'ila Katan, shugaban wata kungiya mai suna ASETEN, wadda ke yaki da sa yara ayyukan karfi, ko ci da guminsu.

Haka nan masu saurare ma sun bugo waya, domin ba da tasu gudummawa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti