Najeriya da China sun kulla yarjajeniya kan man petur

Bututun mai a Najeriya
Image caption Bututun mai a Najeriya

Babban kamfanin mai na Najeriya, NNPC tare da wani kamfanin kasar China, sun sanya hannu akan wata yarjejeniyar gina matatun man fetur uku a Najeriyar, a kan kudi fiye da dala biliyan ashirin.

A cikin yarjejeniyar, wadda ita ce mafi girma da Chinar ta sanyawa hannu a Afirka, kamfanonin biyu sunce za su gina matatun man fetur din ne, don magance matsalar karancin man fetur a Najeriyar, wadda ta ki ci ta ki cinyewa.

A baya dai babban kamfanin man fetur na Najeriyar ya yi ta kokarin shawo kan lamarin, amma hakan ya faskara.

Ana zargin cewa, matsalar cin hanci da rashawa ta jefa matatun man Najeriyar a cikin yanayi marar kyau.