Goodluck Jonathan ya kai ziyara Niger Delta

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jahar Rivers.

Wannan ce ziyarar farko da shugaban ya kai a yankin nasa na Niger Delta mai arzikin mai, tun bayan da ya dare kan kujerar mulki a makon da ya wuce, bayan rasuwar shugaba Umaru Musa 'Yaradua.

Ana sa ran shugaba Goodluck Jonathan zai kaddamar da wasu ayyukan gwamnatin jiha da na tarayya a jahar ta Rivers, da kuma aza harsasan gudanar da wasu.

An kuma ce shugaban zai gana da shugabannin yankin na Niger Delta, musamman kan batun shawo kan matsalar 'yan gwagwarmaya, tun bayan ahuwar da marigayi 'Yaradua ya yiwa wadanda suka ajiye makamai.