An kama madugun 'yan adawa a Sudan

Shugaba Omar al Bashir
Image caption Shugaba Omar al Bashir: Kafin dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu, al Turabi jigo ne a gwamnatin al Bashir

Iyalan fitaccen dan siyasar adawar nan na kasar Sudan, Hassan al Turabi, da ma wadansu manyan jami'an jam'iyyarsa, sun bayyana cewa jami'an Hukumar Tsaro ta kasar sun je gidansa sun tafi da shi cikin dare jiya Asabar.

Kokarin jin ta-bakin hukumomin Sudan din dai ya ci tura, to amma uwargidan Mista Turabi ta shaidawa BBC cewa ta yi amanna an kama shi ne saboda wata kasida da ya rubuta a wata jarida, wadda a ciki ya ce an tafka magudi a zaben da aka gudanar watan jiya.

'Yan adawa da dama dai sun ce sun hakikance an tafka magudi a zaben.

Shi dai Shugaba Omar al Bashir ya lashe kashi sittin da takwas cikin dari na kuri'un da aka kada; jam'iyyarsa kuma ta lashe kusan dukkan kujerun 'yan majalisar dokoki daga arewacin kasar.

A baya dai Mista Turabi ya kasance kusa a gwamnatin kasar ta Sudan kafin dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da Shugaba al Bashir.

Mista Turabi dai na da karfin fada-a-ji a fagen siyasar kasar, an kuma yi amanna cewa shi ne ummul haba'isin juyin mulkin da ya dora Shugaba al Bashir din a kan kujerar mulki a shekarar 1989.

Bayan sun bata da shugaban kasar ne Mista Turabi ya kirkiri tasa jam'iyyar don yin adawa da Shugaba al Bashir.

A shekaru ashirin din da suka gabata ya yi zaman kaso a lokuta daban daban.

Jam'iyyar Shugaba al Bashir dai ta zargi Mista Turabi da goyawa kungiyar 'yan tawayen Darfur ta Justice and Equality Movement (JEM) baya, zargin da Mista Turabin ya sha musantawa.