Tashin hankali a Thailand ya bazu

Wani mai kin jinin gwamnati
Image caption Wani mai kin jinin gwamnati na gujewa wurin da sojojin Thailand suke bude wuta a kan masu zanga-zanga.

Rahotanni sun nuna cewa tashin hankalin da ake yi a Bangkok, babban birnin kasar Thailand, ya bazu zuwa wadansu sassan birnin, yayin da sojoji ke kokarin shawo kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Mutane ashirin da hudu ne dai aka kashe tun da aka fara gwabzawa tsakanin sojojin da masu kin jinin gwamnati ranar Alhamis.

Sojojin gwamnatin dai suna bi titi-titi ne suna kokarin tabbatar da ikonsu, amma hakan na kaiwa ga jikkata karin wadansu mutanen.

Firayim Ministan kasar ta Thailand, Abhisit Vejjajiva, ya ce ba-gudu-ba-ja-da-baya a fito-na-fiton da ake ci gaba da yi.

Firayim Ministan ya kuma ce amfani da karfi ne kadai hanyar da ta rage ta samar da zaman lafiya.