An gabatar da sunan sabon mataimakin shugaban kasa

Architect Namadi Sambo
Image caption Mutumin da aka mika a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa

Majalisar dokokin Najeriya ta tabbatar da cewa, fadar shugaban kasa ta aike mata da sunan Gwaman Jahar Kaduna, Architect Namadi Sambo, a matsayin mutumen da take son ya zama mataimakin shugaban kasar.

Wannan shine karo na farko a tarihin siyasar Najeriyar da 'yan majalisar kasar zasu tantance mutumin da ke son rike mukamin mataimakin shugaban kasa.

Majalisar dokokin ta ce gobe zata yi aikin tantancewar, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.

Idan har majalisar dokokin ta amince da bukatar fadar shugaban kasa, za a rantsar da Architect Namadi Sambo a matsayin mataimakin shugaban kasa.