Taron kasa da kasa a Kamaru kan nahiyar Afrika

Shugaba Paul Biya na Kamaru
Image caption Shugaba Paul Biya na Kamaru

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya bude wani taro na kwararru, wadanda zasu shafe kwanaki biyu suna nazari a kan hanyoyin da ya kamata a bi, domin tsamo nahiyar Afirka daga koma bayan da take fuskanta.

Kwararrun da suka hada da 'yan siyasa da jami'an diplomasiyya, za su yi bitar irin albarkatun da nahiyar Afirkan ta kunsa, sannan su binciko irin abubuwan da ke tauye ta, domin a magance su.

Wasu daga cikin matsalolin dake addabar kasashen Afrika dai sun hada da yake-yake da cucuttuka da tsananin tallauci da rashin ilimi da fari da canjin yanayi da kuma yunwa.

An dai shirya taron ne a wani bangare na bukukuwan cika shekaru hamsin da kasar ta Kamaru ta samu 'yancin kai.