Harin Bom ya kashe mutane 18 a Kabul

Harin Kabul
Image caption Irin asarar da harin na Kabul ya haifar

Wani harin kunar bakin wake da aka kai Kabul babban birnin Afghanistan, yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla sha takwas, ciki har da sojojin Amurka biyar, yayinda wasu mutane hamsin suka jikkata.

Mai magana da yawun sojojin Amurka ya ce biyar daga cikin sojoji biyar din da suka mutu Amerikawa ne, sai dai yawancin wadanda harin ya ritsa da su fararen hula ne.

An kai harin ne akusa da ginin majalisar dokokin kasar da sauran gine-ginen gwamnati. Kuma tuni kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin.

Jami'an 'yan sanda suka ce maharin ya tuka wata mota ne makure da bama bamai, sannan ya nufi hedkwatar kungiyar tsaro ta NATO, akalla motocin NATO biyar ne da kuma na sauran jama'a harin ya lalata.

Image caption Taswirar birnin Kabul wanda ke fama da hare-haren

Shugaba Hamid karzai na kasar ya ce mata da kananan yara 'yan makaranta na cikin wadanda suka hallaka sakamakon harin.

Wani da ya shaida abinda ya faru Obaidullah Saddiqyar, ya ce yana kan hanyarsa ta aiki lokacin da bom din ya tashi, sannan ya bayyana yanayin da cewa yana cike da rudu.

Ya gayawa BBC cewa: " Yace a gaba na bom din ya tashi a safiyar yau da misalin 8 da minti 15, anyi gaba da mutane da dama zuwa asibiti.

"Daga cikin wadanda abin ya ritsa da su har da mata da kananan yara, wadanda aka shaidamin cewa suna kan hanyarsu ne ta zuwa jami'a. Na kuma ga daya daga cikin abokanai na cikin jini a motar 'yan sanda," a cewarsa.

Ya kara da cewa yanayin ya ba shi tausayi sosai har saida nayi kuka, musamman ganin yadda abin ya ritsa da wadanda basu ji ba basu gani ba.

Wadanda aka kaiwa harin

Wakilin BBC a Kabul ya ce, harin wanda shi ne mafi muni cikin watanni da dama, ya nufi jerin gwanon motocin NATO ne, ganin cewa an kai harinne a babbar hanyar yammacin birnin a lokacin da jama'a suka fi hada hada.

Daya daga cikin likitocin da suke kula da wadanda suka jikkata Dakta Shahabi, ya shaidawa BBC cewa, "an kwantar da mutane 37 kawo yanzu, takwas daga cikinsu na mawuyacin hali kuma an yi musu tiyata, sai dai tuni wani yaro da wata mata suka rigamu gidan gaskiya".

Tuni dai aka tsaurara wuraren bincike a birnin na Kabul sakamakon irin wadannan hare-hare, amma sai dai ba kowacce mota ake iya bincika ba, abinda yasa zai yi wuya a iya kawo karshen irin wadannan hare-hare.

A gefe guda sojoji na ci gaba da shirya sabbin hare hare da za a kai kudancin Kandahar, inda kungiyar Taliban keda karfi sosai.

A farkon shekaran nan ne sojojin NATO da na Afghanistan suka kaddamar da wani gagarumin hari kan masu tada kayar baya a yankin Helmand, kuma har yanzu jami'an tsaro na ci gaba da kai farmaki.

Kungiyar NATO da Amurka sun tura karin dubban sojoji zuwa Afghanistan, kuma ana saran adadin zai karu da dubu 15 nan da watan Agusta, a wani mataki na yunkurin kawo karshen tada kayar baya a kasar.