Majalisar dokokin Nijeriya ta amince da Namadi Sambo

Sabon mataimakin shugaban Nijeriya
Image caption Sabon mataimakin shugaban Nijeriya

Majalisun dokokin Najeriya biyu sun tabbatar da zaben gwamnan jihar Kaduna, Architect Namadi Sambo, a matsayin mataimakin shugaban kasar.

A majalisar wakilai, sai da aka dan jinkirta tabbatarwar na kusar rabin saa guda, saboda wasu 'yan majalisar na kiran a dage tabbatarwar har sai an tuntubi masana shari'a sun bada shawara a kan hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da shi.

Shugaba Goodluck Jonathan ne ya mikawa majalisar sunan Alhaji Namadi Sambo, a matsayin wanda yake son ya zama mataimakinsa.

Gwamnan jihar Kadunan zai cike gurbin da Dokta Goodluck Jonathan ya bari ne, bayan ya zama shugaban Nijeriyar, sakamakon rasuwar shugaba Umaru Musa 'Yar adua.

Abinda ya rage a yanzu shi ne rantsar da Alhaji Namadi Sambo kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Cancanta

Wasu da dama na ganin Namadi Sambo a matsayin wanda bai cancanci mukamin ba.

Editan BBC na Abuja Ahmed Idris, ya ce Namadi Sambo ba fitacce bane a siyasance, kasancewar ba a sanshi ba kafin ya zamo gwamna, kuma sunansa ba ya cikin wadanda aka saran za a zaba tun farko.

Har ila yau ana ganin shugaban ya zabe shi ne domin ba shi da gogewar da zai iya kawo masa kalubale a siyasance.

Yayinda wasu ke ganin wani sabon salo ne na tafiyar da al'amura da shugaban ke son fitowa da shi.

Zaben shekara ta 2011

Har yanzu dai babu tabbas ko shugaba Jonathan zai tsaya takara a zaben shekarar 2011 ko kuma a'a.

A makon da ya gabata an ruwaito daya daga cikin masu yi masa hidima, yana cewa shugaban zai tsaya takarar, amma daga bisani ya janye zancen nasa, yana mai cewa ba haka yake nufi ba.

Ita dai jam'iyyar PDP ta ce dan takarar ta zai fito ne daga Arewacin kasar, saboda yarjejeniyar da ta cimma ta raba iko tsakanin yankunan kasar.

Amma ana hasashen Jonathan zai yi kokarin kaucewa wannan yarjejeniya domin ci gaba da mulki.

Baya da kura

Rahotanni daga jihar Kaduna inda namadi ke gwamna sun nuna cewa, nadin Namadin a matsayin mataimakin shugaban Najeriya ya bar baya da kura.

A yanzu dai mataimakinsa Mr. patrick Yakowa wanda Kirista ne, shi zai gaji kujerar gwamnan jihar.

Hakan dai kamar yadda rahotanni suka nuna, ya fusata jama'a da dama a jihar, saboda Musulmi ne suke da rinjaye a jihar.

Sabon mataimakin shugaban kasar dai na da aure, da 'ya'ya shida, kuma kwararre ne a harkar zane zanen gine-gine.