Majalisa za ta tantance Namadi Sambo

Ach Namadi Sambo
Image caption Ach Namadi Sambo wanda ake sa ran zai zama mataimakin shugaban kasa

A Najeriya, yau ne ake saran Majalisar wakilan kasar za ta tantance gwamnan jihar Kaduna Architect Muhammed Namadi Sambo a matsayin mataimakin shugaban kasar.

Hakan dai ya biyo bayan mika sunansa ne da shugaban kasar Dr. Goodluck Jonathan yayi wa majalisun dokokin kasar don neman a tantance shi kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

Wannan dai shi ne karon farko da Majalisar dokokin Najeriyar za ta tantance wani a matsayin Mataimakin shugaban kasar.

Zaben Namadi Sambon dai a matsayin Mataimakin shugaban kasar ya janyo kace nace musaman ma a jihar sa ta Kaduna.