Hukumar NDLEA ta kama wani dan siyasa

Taswirar Nigeria
Image caption Nigeria ta dade ta na yaki da fataucin miyagun kwayoyi.

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nigeria NDLEA, ta ce ta kama wani dan siyasar kasar a bisa zarginsa da yunkurin fasakaurin hodar iblis a filin jirgin saman Murtala Mohammed dake Lagos.

Jami'ai a hukumar sun ce ya hadiye kusan kilo biyu na hodar ta iblis domin samun kudadenda zai yi amfani da su a yakin neman zabensa.

Dan siyasar mai shekaru 52 a duniya, wato Eme Zuru Ayortor, na takarar kujerar majalisar jiha ne a jihar Edo.

Jami'an hukumar sun ce ya shaidawa masu cewar, yana matukar bukatar kudin ne, domin takarar da yayi a shekarar 2007 ta talauta shi.