Taimakon dala billion 25 ga kasar Girka

Shugaban kasar Girka da takwaransa na kasar Turkiyya
Image caption Prime Ministan Girka George Papandreou da takwaransa na kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan

Tarayya turai ta ce a yau talata ne kasar girki zata fara karbar kashin farko na kudaden da aka shirya bata rance don shawo kan matsalolin basussukan da suka dabaibaye kasar.

Adadin farko na dala billion 25, ka iya kasancewa taimakon gwamnati da aka fara bayarwa ga wata kasa mafi girma a tarihi wanda za a baiwa kasar ta Girka.

Kasashen dake amfani da kudin euro tare da asusun bada lamuni na duniya, su ne manyan masu bada tallafin na kimanin dala trillion guda.

A halinda ake cikin dai, darajar kudin na euro na ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya.