Hukumar EFCC ta fara bincike kan badakalar Siemens

Hedikwatar kamfanin Siemens
Image caption Ana zargin kamfanin Siemens da bayar da toshiyar baki

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'anati a Najeriya, EFCC ta ce ta fara gudunar da bincike kan batun kamfanin sadarwa na Siemens.

Ana zargin kamfanin na kasar Jamus ne da bada kudi fiye da euro miliyan goma sha bakwai ga wasu yan najeriya da suka taba rike mukaman gwamnati a shekarun da suka gabata a matsayin toshiyar baki .

Shugabar hukumar Madam Farida Waziri ce ta sanar da haka a wani taron manema labari a Abuja.

Madam Farida Waziri ta ce ta gayyaci tsaffin ministocin sadarwa na kasar guda hudu zuwa ofishinta domin amsa wasu tambayoyi dangane da wannan batu.