Sabbin takunkumi akan Iran

Nuclear kasar Iran
Image caption Amurka ta yi biris da yarjejeniyar da Tehran ta amince da shi

Amurka ta gabatar da wani kudurin MDD na sanya sabbin takunkumi akan kasar Iran, inda ta yi biris da yarjejeniyar da Tehran ta amince da shi a baya.

Kudurin zai haramta aiyukan soji da na harkokin kudi da na jiragen ruwa wadanda ke da alaka da shirin Nuclear kasar Iran, wanda kasashen yammacin duniya ke zargin cewa ana sarrafawa ne domin kera makamai, zargin da Iran ta musanta da babbar murya.

Kudurin ya hadu ne bayan tsawon makonni ana kai ruwa rana tsakanin mambobi 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na MDD da kasar Jamus.

A yanzu da suka amince da rubutaccen kudurin, su na nema sauran mambobin kwamitin sulhun guda 15 su amince da shi.