NAPTIP ta yi wa Sen Yarima tambayoyi

Senata Sani Yarima
Image caption Hukumar NAPTIP ta yiwa Sanata Yarima tambayoyi

Hukumomi a Najeriya sun ce sun yi wa tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmed Sani tambayoyi bisa auren wata yarinya da yayi da ake zargin cewa bata tasa ba.

Sanata Yarima ya tabbatar wa da jami'an Hukumar yaki da safarar bil'adama da laifuka makamantan haka a kasar wato NAPTIP cewa ya auri wata yarinya amma ya ki ya tabbatarwa da Jami'an cewa shekarun ta na haihuwa dududu basu wuce sha uku ba.

A wata hira da BBC a kwanakin baya, Sanata Ahmed Sani ya ce babu laifi a auren da yayi a matsayinsa na Musulmi mai bin dokokin addinin Musulunci.

A jiya ne dai hukumar ta gayyaci Sanatan zuwa ofishinta inda ta ce tayi masa tambayoyi akan auren nasa amma daga bisani ta bada belinsa har zuwa ranar 17 ga watan gobe domin ya sake bayyana a gabanta.