'Yan sandan Najeriya na ci gaba da keta hakkin Jama'a

'Yan sandan Najeriya
Image caption 'Yan sandan Najeriya sun dade suna fuskantar zargin cin zarafin jama'a

Wani rahoto da gamayyar kungiyar Civil Liberties ta gabatar ya ce 'yansanda a Najeriya na ci gaba da kisan gilla da azabtar da mutanen da suke tsare da su da kuma yiwa mata fyade.

Rahoton ya ce 'yan sanda kan gabatar da masu laifi ga manema labarai sannan su kashe su daga bisani ba tare da yi musu shari'a ba.

Wannan rahoton wanda kungiyar Open Society Justice Initiative ta jagoranta, shi ne na baya-bayannan da ya zargi 'yan sandan Najeriyar da laifin cin zarafin jama'a da kuma cin hanci da rashawa.

Sai dai kawo yanzu mahukunta a kasar ba su maida martani game da wannan rahoto ba.

Yadda aka aiwatar da binciken

Kungiyar tace ta shafe fiye da shekaru biyu tana tattaunawa da jami'ai da kuma wadanda ake zargi a ofisoshin 'yan sanda 400.

"'Yan sanda a Najeriya na yiwa jama'a kisan gilla da cin zarafi nawa, ba tare da la'akari da doka ba," kamar yadda rahoton ya ce. Rahoton ya kara da cewa 'yan sandan Najeriya kan kashe jama'a a lokuta daban daban kan jama'ar da ake zargi da aikata laifuka. Rahoton ya bayyana yadda ake gudanar da kashe-kashe ba bisa ka'ida ba, sannan a batar da mutane.

Karuwai

Rahoton ya kuma bayyana yadda ake kama karuwai ana yi musu fyade.

An rawaito wani dan sanda yana cewa: "Yana daya daga cikin alfanun da ke tattare da sunturin da muke yi cikin dare".

Wasu karuwai a Legas sun shaidawa BBC cewa rahoton kungiyar gasikiya ne.

"Tace sun kamo mu, sannan suka nada mana duka.... suka yi mana fyade ba tare da kwaroron roba ba". A cerwar wata karuwa a Legas

" A wani lokacin sukan caje mu, su sace mana kudaden mu, sannan su yarda mu su gudu". Ana kuma tilastawa mata su bada kawunansu a matsayin beli a ofisoshin 'yan sanda.

Wasu karuwan sun bayyana yadda mutane cikin kayan sarki kan kai musu hari - wadanda alamu ke nuna cewa sun fito ne daga yankunan su.

Daukar mataki

An dade ana allawadai da yadda 'yan sanda ke gudanar da ayyukansu akasar. An kuma kafa kwamitoci da dama domin duba yadda za a inganta ayyukan 'yan sanda a kasar.

A shekara ta 2004 ne aka fara yunkurin kawo sauyi a kan daftarin ayyukan 'yan sanda, amma kudurin na wucin gadi na nan a ajiye tun shekara ta 2006.

A 'yan kwanakinnan 'yan sandan Najeriya na amfani da irin wadannan kalmomi domin farfado da kimarsu " dan sanda abokin kowa", sai dai ba duka 'yan kasar ne suka yi imani da wannan ba.