Ana musayar wuta a Thailand

Zanga zanga a Thailand
Image caption Dakarun dake arangama da masu zanga zanga a kasar thailand

Ana musayar wuta na albarusai tsakanin masu zanga zangar adawa da gwamnati da suka kafa sansani a cibiyar Bangkok, babban birnin kasar Thailand.

Gwamnatin kasar ta ce za ta tura dakarun hadin gwiwa zuwa yankin.

A kalla mutane biyu suka rasu yayinda da dama Suka jikkata.

Matsa kaimi kan masu zanga zangar ya biyo bayan wa'adin ranar Litinin ne da gwamnatin kasar ta debarwa masu zanga zangar, sannan yunkurin samun maslaha ta hanyar tattaunawa ya ci tura a jiya talata.

Wakiliyar BBC ta ce dakarun sojin sun kusa rusa wani shinge da masu zanga zangar suka kafa.