An dage dokar hana fita a Jos, Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Gwamnati ta ce zaman lafiya mai dorewa ya samu a Jos

A Najeriya, gwamnatin Jihar Filato ta bayar da sanarwar dage dokar hana fitar daren da ta sanya a Jos, babban birnin jihar, da kewaye, bayan rikicin da ya barke a watan Janairu, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama da dukiyoyi masu dimbin yawa.

Gwamnatin jihar Filaton dai ta dauki wannan mataki ne a daidai lokacin da wadansu ke ganin har yanzu akwai sauran aiki dangane da wanzar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

A kwanakin baya dai an yi ta samun rahotannin kisan mummuke a wadansu sassan birnin na Jos da kewaye.

Sai dai kakakin gwamnatin jihar ta Filato, Mista Dan Manjang, ya shaidawa BBC cewa ikirarin da wadansu ke yi cewa har yanzu ana zaman dardar a wasu sassan jihar hasashe ne kawai na wadanda ba sa son ganin jihar ta zauna lafiya.

“Idan ka zo Jos za ka ga cunkoson jama’a; muna tabbatarwa duniya [cewa] zaman dardar [din] da ake cewa [akwai] hasashe ne kawai wanda mutanen da ba sa son su ga mun ci gaba [suke] ta yadawa.

“Mu a jihar Filato, yanzu mun riga mun rungumi juna, mun zama al’umma daya, mun fahimci juna, mun yarda kuma za mu zauna tare”, inji Mista Manjang.

Gwamnatin ta dage wannan dokar hana fitar daren ne dai bayan wata ganawa da majalisar tsaro ta jihar ta yi jiya Laraba, inda ta yanke shawarar cewa “zaman lafiya mai dorewa ya samu a jihar”.