Korea ta Arewa ta karyata zargin nutsar da Jirgin ruwa

Jirgin ruwan yakin Korea ta Kudu
Image caption Jirgin ruwan yakin mai suna Cheonan ya nutse ne bayan wata nakiya ta dake shi

Rundunar sojin Koriya ta Arewa ta ce zargin da ake yi ma ta cewar ita ta nutsar da wani jirgin ruwan yaki na Koriya ta Kudu, kage ne kawai, ta kuma nemi a nuna ma ta shaida.

A wata sanarwa da ba kasafai ake irinta ba, hukumar tabbatar da tsaro ta kasa, wadda ta fi kowace karfin fada-aji, ta yi barazanar daura yaki, kan duk wata takala da aka yi ma ta, ta fuskar soji.

Kafar yadar labaran Koriya ta arewan kenan, tana cewa, hukumar tsaron kasar zata tura wata tawaga ta masu sa ido, zuwa Koriya ta Kudu, domin gane ma idanunta hujjojin da aka yi amfani da su wajen danganta kasar da nutsar da jirgin ruwan.

Kafin haka dai,Koriya ta Kudu ta nuna abin da ya rage na makamin da aka yi amfani da shi wajen nutsar da jirgin ruwan da ya haddasa mutuwar mutane arba'in da shidda.

Amurka ta ce tana goyon bayan rahoton masu bincike da ke cewa Korea ta Arewa ce ta kai hari a kan wani jirgin ruwan yaki na Korea ta Kudu, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane arba'in da shida.

Tun farko dai wata sanarwa daga fadar gwamnatin Amurkan ta White House ta bayyana harin da cewa takalar fada ce, hakan kuma zai kara mai da Korea ta Arewan saniyar ware.

Sanarwar ta kuma jaddada bukatar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, duk kuwa da bayyana harin a matsayin tsokanar fada da ta yi.

A cikin sanarwar ta White House dai babu maganar daukar fansa: Amurka ba za ta so ta ga fada ya barke a yankin ba.

A cewar masana, Amurkan za ta nemi hanyoyin mayar da martani ne da za su hana aukuwar irin wannan al’amari nan gaba a maimakon ta fusata Korea ta Arewan.

Wadansu majiyoyi a Washington sun bayyana cewa gwamnatin Obama na duba yiyuwar sake shigar da sunan Korea ta Arewa cikin jerin kasashen da ke renon ta'addanci bayan cire sunan nata da aka yi a shekarar 2008; hakan kuma na nufin kakabawa Korea ta Arewan takunkumi.

Rahoton masu binciken, wanda Korea ta Kudu ta wallafa, ya zargi Korea ta Arewa da laifin nutsar da jirgin ruwan yakin mai suna Choenan, ta hanyar amfani da wani makami da aka harba daga karkashin teku.

Wadanda suka rubuta rahoton dai sun hada ne da masana daga kasashen waje, kuma sun wallafa rahoton ne bayan sun nazarci bangaren jirgin ruwan da ya balle.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, za ta kai ziyara kasashen Japan da Korea ta Kudu da China a ’yan kwanaki masu zuwa.

Babu shakka kuma za ta fi mayar da hankali ne a kan wannan sabon rikicin da ya ke kunno kai tsakaknin kasashen Korea ta Arewa da ta Kudu.