Sunan jam'iyyar 'yan adawar Najeriya

A Najeriya, kungiyar 'yan adawar kasar ta National Democratic Movement, wato NDM, ta sanar da sunan sabuwar jam`iyyar da ta ke kokarin kafawa domin kalubalantar jam`iyyar PDP mai mulkin kasar a zaben shekara ta 2011.

Sabon sunan da ta rada wa jam`iyyar dai shi ne ACPP, wato Action Congress Party.

Wani kusa a kungiyar ta NDM, Alhaji Umar Dan-Musa Abubakar, ya shaida wa BBC cewa an yanke shawarar rada wannan suna ne don ya dace da jam’iyyun da suka amince su shiga wannan tafiya.

“ACPP din nan jam’yya ce wadda aka dauko sunanta daga jam’iyyu da yawa wadanda aka tattauna da su; ra’ayi ne na jam’a da yawa…”

Shi ma tsohon gwamnan Jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim, ya ce ‘yan jam’iyyar ANPP sun yanke shawarar su shiga a yi wannan tafiya da su ne saboda sun gano in ba hakan suka yi ba, to aikin banza za su yi ta yi.

“Mun gane in ba haka aka yi ba, duk abin da muke yi aikin banza ne; kuma ana kafa jam’iyya ne saboda a ci zabe, shi ya sa muka dawo yanzu za mu hadu gaba daya”.

'Yan jam'iyyar dai sun ce rajistar hukumar zaben kasar kawai suke jira domin shiga a fafata da su a fagen siyasar Najeriya.

Tun farko dai an kafa kungiyar ta NDM ne da nufin hade jam'iyyun adawa a Najeriya don tunkarar zabuka masu zuwa; sai dai kokarin yin hakan ya yi ta cin karo da matsaloli da dama.