An sabunta: 21 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 16:24 GMT

'Yan Niger na gudun hijira zuwa Najeriya

Sojojin Niger

Tunda sojoji suka kwaci mulki suka yi shelar neman taimako

Rahotanni daga arewacin Najeriya na cewa jama'a daga jamhuriyar Niger na kara tsallakawa zuwa kan iyakar kasar da Najeriya saboda karancin abincin da ake fama da shi akasar.

Wakilin BBC a arewacin Najeriya, yace mata da kananan yara daga Niger na neman mafaka a wajen mazauna garin.

Kungiyoyin agaji sun ce akalla mutane miliyan bakwai-kusan rabin al'umar kasar ne-suke fuskantar karancin abinci.

A yanzu dai gwamnatin riko ta kasar ta fara rarraba kayan abinci a arewacin kasar inda lamarin yafi kamari.

Wakilin BBC Abba Muhammad Katsina, yace wasu daga cikin mutanen da suka iso Najeriyana sayar da ruwa da kuma shayi domin samun kudin kashewa.

Yace akwai rahotannin daek nuna cewa mata na shiga gida-gida domin neman taimakon abinci.

A kwai karin rahotannin da ke cewa wasu 'yan kasar ta Niger da dama sun isa jihar Sokoto domin neman kalaci.

Amma shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattawan Najeriya, Sanata Jibril Aminu, ya gayawa BBC cewa zai nemi majalisar ta tattauna akan lamarin idan suka dawo daga hutu.

Yadda ake fama da karancin abinci a Niger

 • Wasu mata a layin karbar abinci
  Hukumar samad da abinci ta duniya WFP ko PAM a takaice, tare da hadin gwiwar gwamnatin Niger, sun fara rarraba kayan abinci mai gina jiki ga miliyoyin 'yan kasar da ke fama da matsalar tamowa.
 • Wasu mata dauke da buhu
  Mata da kananan yara ne ke kan gaba wajen fuskantar matsalar da kididdiga ta nuna cewa za ta shafi 'yan kasar kimanin milyan takwas a wannan shekarar.
 • wasu mata na sayen abinci
  Sai dai yayinda gwamnati da hukumomi ke samar da abinci mai gina jiki a farashi mai rahusa, talauci da rashin abin saye na hana wasu damar sayen abincin da yawa.
 • Wata mata na karbar abinci
  A wasu kauyukan kasar, hukumar sammar da abicin ta majalisar dinkin duniyar WFP, na tallafa wa yara 'yan makaranta da abinci a ajujuwansu domin bunkasa ilimi.
 • Wata mata da danta
  Matsalar karancin abincin dai ba a Nijar kadai ya tsaya ba, har ma da wasu yankuna na makotan kasar kamar arewacin Najeriya, inda karancin abincin ke illa. Idy Baraou ne ya daukar mana hotunan.

Jama'ar gari

Wata mazauniyar garin Zinder, ta shaidawa BBC cewa tana da yarinyar da ke zuwa makaranta, amma ba ta iya samun abinci kullum.

" Tace bani da abincin da zan ci, saboda wannan shekarar bata yi mana kyau ba," a cewar Nana Maryam

Ta kara da cewa bani da abinda zan ci ko na ciyar da 'ya'yana, miji na ya tafi Najeriya domin neman abinci".

Yayinda wani mutum yace ya rasa kimanin rakuma tamanin, yayinda ragowar suka kasa tashi saboda rashin abinci.

Ko a watan daya gabata, sai dai jami'in majalisar dinkin duniya mai kula da jin kai John Holmes, ya gayawa BBC cewa Niger na fuskantar barazanar lalacewar kayan abinci, sannan yace lamarin yafi na shekara ta 2005 kamari.

Sai dai yace gwamnatin kasar na bada hadin kai wajen rabon kayan abincin.

Tsohon shugaban kasar Tandja Mamadou, wanda sojoji suka yiwa juyin mulki awatan Febreru, ya sha suka kan rashin tabuka komai kan lamarin.

Majalisar dinkin duniya tace ana bukatar kimanin dala miliyan 130, domin ciyar da kimanin mutane miliyan takwas din da ke fama da yunwa.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.